Amnesty ta fitar da rahoton shekara kan cin hanci a kasashen duniya
Kungiyar Transparency dake yaki da cin hanci da rashawa a duniya, ta fitar da rahotan ta na shekara shekara, wanda ke nuna kasashen da aka fi samun cin hanci a duniya.
Wallafawa ranar:
Shugaban kungiyar, Delia Ferreira Rubio tace ba’a samu ci gaba a kasashe da dama ba, kan matakan da suke dauka na dakile matsalar cin hanci a cikin shekaru 6 da suka gabata.
Kungiyar tace cin hancin na take hakkokin jama’a da kuma bin doka da oda, wanda ke nuni da dangantaka tsakanin gaskiya da dimokiradiya.
Kungiyar ta bayyana kasashen Senegal, Cote d’Ivoire da kuma Birtaniya a matsayin wadanda suka samu ci gaba, yayin da kasashe irin su Syria da Yemen da ake fama da tashin hankali suka kara samun koma baya.
Kasashen da cin hancin yayi kamari sun hada da Somalia, Sudan ta Kudu, Syria, Afgahnistan, Yemen, Sudan, Libya, Koriya ta Arewa, Venezuela da kuma Iraqi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu