Isa ga babban shafi
Faransa

Macron na fuskantar matsala saboda 'yan cirani a Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na fuskantar matsalar gaske cikin wannan mako game da batun sabuwar doka da za ta tsaurara matakai kan ‘yan ci rani, ganin yadda wasu mambobin jamiyarsa ba sa goyon bayan sabuwar dokar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Zoubeir Souissi
Talla

Bayan da Faransa ta yi nazarin bayanan masu neman mafaka a kasar dubu 100 a  bara, shugaba Macron ya sha alwashin gaggauta duba bukatun masu neman mafaka na hakika, in da ya ce za a yi waje da ‘yan ci ranin da ke neman arziki kawai.

Ana shirin gabatar da sabuwar dokar a gobe Laraba ga Majalisar Ministocinsa, kafin a mika ta ga Majalisar Dokokin Faransan domin tafka muhawara a kai.

A Laraban ne ake ganin ma'aikatan kotun kula da masu bukatar mafaka da kuma ofishin kula da ‘yan gudun hijira za su yi bore saboda wannan sabuwar doka wadda kungiyoyin ma'aikatan ke ganin ta saba wa tsarin neman mafaka a Faransa.

A lokacin da gwamnatin Faransa ke tarwatsa sansanin ‘yan gudun hijira na Calais a shekara ta 2016, matasa daga nahiyar Afrika da kudancin Asiya sun yi ta komawa gabar tekun Birtaniya, wasu kuma suka rika kwana a titunan birnin Paris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.