Isa ga babban shafi
Falasdinu

Falasdinu na neman kujerar mamba a MDD

A wannan Talata shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas zai nemi goyon bayan kasashe domin bai wa Falasdinu cikakkiyar damar kasancewa mamba a Majalisar Dinkin Duniya a wani jawabi da zai gabatar a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas REUTERS/Yves Herman
Talla

Har ila yau a  cikin wannan jawabi, Abbas zai nuna rashin amincewa da Amurka a matsayin wadda za ta jagoranci tattaunawar sulhu tsakaninsu da Isra’ila, in da a maimakon hakan zai nemi Majalisar da ta zama jagora a tattaunawar.

Sai dai ana ganin gwamnatin Isra’ila ba za ta amince da wani mai shiga tsakani ba da ya wuce Amurka, lura da yadda ta ke yawan caccakar Kungiyar Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya bisa zargin su da nuna son-kai.

Hankula za su karkata ne a yau kan Abbas da Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley wadda a ‘yan makwannin da suka shude ta caccaki Abbas tare da fadin cewa, ba shi da karsashin da ake bukata wajan cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

A karo na farko kenan da Abbas zai gabatar da irin wannan jawabin a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya tun shekarar 2009.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.