Isa ga babban shafi
Oxfam

Darektan Oxfam ya yi murabus saboda lalata da karuwai

Tsohon Direktan kungiyar Oxfam a Haiti, Roland van Hauwermeiren ya yi murabus bayan ya shaida wa masu bincike cewa, tabbas ya taba yin amfani da kudin kungiyar wajen hayar karuwai a 2010, lokacin da kungiyar ke aikin agaji ga wadanda girgizar kasa ta shafa a kasar.

Oxfam ta sha caccaka daga sassan duniya saboda zargin da ake yi wa jami'anta na lalata da karuwai a HAiti
Oxfam ta sha caccaka daga sassan duniya saboda zargin da ake yi wa jami'anta na lalata da karuwai a HAiti REUTERS/Simon Dawson
Talla

Mr. Van Hauwermeiren na cikin jami’an kungiyar Oxfam bakwai da aka zarga da yin lalata da karuwan a wani muhalli na kungiyar a Haiti, kuma tuni uku daga cikinsu suka yi murabus, yayin da aka kori hudu.

Bayan tabbatar da laifin da ake zarginsa da aikatawa, Oxfam ta bai wa Mr. Van Hauwermeiren damar sauka daga mukaminsa cikin girma da arziki.

Rahoton ya ce, wadanda aka zarga sun yi barazana ga kananan ma’aikatan da suka yi kokarin bada shaida kan abin da suka aikata a binciken 2011.

Oxfam mai cibiya a Birtaniya ta musanta yunkurin rufa-rufa kan laifin da jami’anta suka aikata a Haitin, yayain da ta yi alkawarin daukan matakin magance matsalar cin zarafin mata, sannan ta ce, za ta bada hakuri ga gwamnatin Haiti kan badakalar.

A watan jiya ne labarin badakalar ya dada fitowa, lamarin da ya matukar shafar kimar kungiyar ta Oxfam bayan ta sha suka daga sassan duniya.

Gwamnatin Birtaniya ta ce, ya zama wajibi ga kungiyar ta samar da sauye-sauye kafin neman izinin karbar kudin haraji.

Oxfam na da ma’aikata kusan dubu 10 da ke aiki a kasashen duniya fiye da 90.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.