Isa ga babban shafi
EU-NATO

EU ta amicewa NATO kan bada tsaro a kasashenta

Kungiyar Tarayyar Turai ta EU ta amince da NATO ita kadai ta ci gaba da aikin bayar da tsaro ga kasashen da ke cikinta. Matakin ya biyo bayan wani taro da ministocin kasashe mambobi a kungiyar ta NATO suka gudanar a yau a birnin Brussels na Belgium da ya nuna damuwarsa game da wata hadakar kawance kan sha’anin tsaron yankin da EU ta kaddamar a watan Disamban bara.

Wasu daga cikin dakarun tsaro na NATO
Wasu daga cikin dakarun tsaro na NATO U.S. Army/Sgt. Stephen A. Gober/Handout via Reuters
Talla

Bayan wata ganawa da Ministar Harkokin Wajen Kasashen Kungiyar Tarayyar Turai Federica Mogherini, Sakataren Harkokin Tsaron Amurka, James Mattis ya ce,  NATO ce kadai ke da hakkin bayar da kariyar tsaro ga kasashen kungiyar 29.

A cewar Mattis ba dai dai ba ne a amince wa wasu kasashen Turai su samar da wata kungiya da za ta yi makamancin aikin da NATO ke yi, in da ya ce, za su ci gaba da karfafa ayyukan NATO a ilahirin kasashen.

Shi ma babban Sakataren Kungiyar Tsaron ta NATO, Jens Stoltenberg ya yi maraba da matakin kungiyar ta EU, yana mai cewa ba shi da yakinin hadakar dakarun kawancen da aka kaddamar cikin watan Disamban baran za ta iya wani aikin katabus a sha’anin tsaron Turai.

Tun bayan yakin duniya na biyu ne kasashen Turai 22 da kuma wasu 6 da ba na Turai ba da suka kunshi Iceland da Norway da Albania da Montenegro da Turkiya da Amurka da kuma Canada, suka kafa kungiyar hadakar jami’an tsaron ta NATO don bayar da kariya a yankunansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.