Isa ga babban shafi
Myanmar

"Myanmar ta gaza daukan mataki kan 'yan Rohingya"

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, gwamnatin Myanmar ta gaza wajen samar da matakan da suka dace domin ganin 'yan kabilar Rohingya dubu 688,000 da aka tantance a Bangladesh sun koma gida.

Musulman Rohingya da ke fakewa a Bangladesh
Musulman Rohingya da ke fakewa a Bangladesh REUTERS/Tyrone Siu
Talla

Kwamishinan kula da 'yan gudun hijira a Majalisar Dinkin Duniya, Filippo Grandi ya shaida wa taron Kwamitin Sulhu na Majalisar cewar, babu wani ingantaccen shiri da yanzu haka ke kasa dangane da komar 'yan gudun hijirar gida.

Grandi ya ce, ba a magance abin da ya raba su da matsuguninsu ba, kuma babu wani shiri daga gwamnatin Myanmar da ke nuna cewar za a daina nuna mu su wariya da kuma gallazawar da ake yi mu su a matsayin 'yan kasa.

Dama daga cikin mutanen Myanmar mabiya addinin Bhuda na kallon Musulman Rohingya tsiraru a matsayin bakin da ba su da cikakken 'yanci a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.