Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Yau ce ranar rediyo ta duniya

Yau ita ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin yin dubi dangane da muhimmancin rediyo a tsakanin al’umma, lura da irin yadda milyoyin mutane suka dogara da rediyo domin shakatawa da kuma sanin halin da duniya ke ciki.

Miliyoyin mutane a sassan duniya syn digara da rediyo wajen samun labaran duniya
Miliyoyin mutane a sassan duniya syn digara da rediyo wajen samun labaran duniya RFI/Anthony Fouchard
Talla

Duk da irin ci gaban da aka samu ta bangaren kimiya da kuma yada labarai, rediyo na ci gaba da kasancewa daya daga cikin hanyoyi mafi sauki wajen isar da sakwanni a tsawon zamuna.

Babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya jaddada hakan a sakon da ya aike da shi dangane da zagayowar wannan rana, in da ya ce,

“Rediyo, na a matsayin kafar yada labarai da ta fi saukin isa ga jama’a a duniya. Duk da irin sauyin da aka sama ta fannin kimiya, amma har yanzu rediyo na ci gaba da rike matsayinsa na shakatarwa, wayar da kai da kuma ilmantarwa.”

Guterres ya kara da cewa, “Rediyo na hada kawunan jama’a da kuma kasancewa muryar wadanda ake tauye wa hakkokinsu. A shekarar bana, mun yi la’akari da yadda labaran wasanni ke a matsayin wata hanyar shakatarwa da kuma cimma wasu muradu na jama’a.”

Ko baya ga isar da sakwanni a cikin sauki, rediyo, ya zama jigo musamman ta fannin hada kawunan jama’a da kuma sada zumuci, kamar dai yadda shugabar hukumar bunkasa ilimi, kimiya da kuma tattalin al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO Audrey Azoulay ta bayyana.

Jami’ar ta ce, “Rediyo na kasancewa wata dama da ke hada jama’a da kuma kulla abokantaka, shi ne na farko wajen yaki da bambancin wariyar launin fata ko na jinsi a tsakanin al’umma, sannan kuma yana taimakawa wajen samar da daidaito a tsakanin maza da mata.”

Hukumar UNESCO na ci gaba da aiki tukuru domin habbaka harkar rediyo wajen yada al’adu kamar yadda Azoulay ta tabbatar, in da kuma ta ce, ya kamata a yi aiki kafada-da-kafada domin tattaunawa, ci gaba, da kuma samar da zaman lafiya ga kowa da kowa.

To ko yaya duniya za ta kasance idan aka wayi gari ba tare da rediyo ba?

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.