Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 15/02 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 10/02 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 10/02 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 15/02 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 15/02 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 10/02 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 10/02 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 15/02 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 10/02 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 15/02 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 10/02 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 10/02 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 15/02 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 10/02 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 15/02 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 15/02 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 10/02 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 10/02 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 15/02 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Gaggauce

Rahotanni daga Najeriya, na cewa hukumar shirya zabe INEC, na ganawa da masu ruwa da tsaki, jami'an sa ido kan zabukan kasar na cikin gida da na kasashen ketare, dangane da yiwuwar dage zaben shugaban kasa da 'yan majalisun dokokin tarayyar kasar na ranar 16 ga watan Fabarairu. Babu cikakken karin bayani kan dalilan da suka haddasa wannan taro na gaggawa, sai dai wata majiya ta ce rashin isar kayayyakin aikin zabe zuwa wasu yankuna na daga cikin batutuwan da ka 'iya haddasa sauya ranar zabukan.

Duniya

Yau ce ranar rediyo ta duniya

media Miliyoyin mutane a sassan duniya syn digara da rediyo wajen samun labaran duniya RFI/Anthony Fouchard

Yau ita ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin yin dubi dangane da muhimmancin rediyo a tsakanin al’umma, lura da irin yadda milyoyin mutane suka dogara da rediyo domin shakatawa da kuma sanin halin da duniya ke ciki.

Duk da irin ci gaban da aka samu ta bangaren kimiya da kuma yada labarai, rediyo na ci gaba da kasancewa daya daga cikin hanyoyi mafi sauki wajen isar da sakwanni a tsawon zamuna.

Babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya jaddada hakan a sakon da ya aike da shi dangane da zagayowar wannan rana, in da ya ce,

“Rediyo, na a matsayin kafar yada labarai da ta fi saukin isa ga jama’a a duniya. Duk da irin sauyin da aka sama ta fannin kimiya, amma har yanzu rediyo na ci gaba da rike matsayinsa na shakatarwa, wayar da kai da kuma ilmantarwa.”

Guterres ya kara da cewa, “Rediyo na hada kawunan jama’a da kuma kasancewa muryar wadanda ake tauye wa hakkokinsu. A shekarar bana, mun yi la’akari da yadda labaran wasanni ke a matsayin wata hanyar shakatarwa da kuma cimma wasu muradu na jama’a.”

Ko baya ga isar da sakwanni a cikin sauki, rediyo, ya zama jigo musamman ta fannin hada kawunan jama’a da kuma sada zumuci, kamar dai yadda shugabar hukumar bunkasa ilimi, kimiya da kuma tattalin al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO Audrey Azoulay ta bayyana.

Jami’ar ta ce, “Rediyo na kasancewa wata dama da ke hada jama’a da kuma kulla abokantaka, shi ne na farko wajen yaki da bambancin wariyar launin fata ko na jinsi a tsakanin al’umma, sannan kuma yana taimakawa wajen samar da daidaito a tsakanin maza da mata.”

Hukumar UNESCO na ci gaba da aiki tukuru domin habbaka harkar rediyo wajen yada al’adu kamar yadda Azoulay ta tabbatar, in da kuma ta ce, ya kamata a yi aiki kafada-da-kafada domin tattaunawa, ci gaba, da kuma samar da zaman lafiya ga kowa da kowa.

To ko yaya duniya za ta kasance idan aka wayi gari ba tare da rediyo ba?

Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure