Isa ga babban shafi
Rasha

Ana bincike kan mutuwar mutane 71 a jirgin Rasha

Masu gudanar da bincike a Rasha na karade wurin da jirgin saman fasinjan kasar ya yi hatsarin da ya sabbaba mutuwar daukacin mutane 71 da ke cikinsa a kusa da birnin Moscow.

Dusar kankara ta lullube jirgin da ya hatsari a yankin Ramensky na Rasha a ranar Lahadi
Dusar kankara ta lullube jirgin da ya hatsari a yankin Ramensky na Rasha a ranar Lahadi REUTERS/Stringer
Talla

Jirgin fasinjan samfurin Antonov An-148 ya gamu da hatsarin ne bayan ya taso daga filin jiragen sama na Domodedovo da ke birnin Moscow da zimmar isa birnin Orsk amma ya yi hatsari a yankin Ramensky.

Masu bincike sun bayyana hatsarin a matsayin daya daga cikin munanan hatsurran jiragen sama da aka gani a tarihin Rasha.

Fasinjoji 65 da kuma jami’ai shida ne ke cikin jirgin, kuma dukkaninsu sun riga mu gidan gaskiya kamar yadda hukumomin Rasha suka tabbatar.

Dusar kankara ta lulllube yankin da hatsarin ya auku, lamarin da ya haifar da jibin goshi ga jami’an agajin gaggawa kafin su isa yankin.

A ‘yan makwannin nan dai, Rasha na fama da matsannaciyar zubar kankara, yayin da masu bincike ke cewa, ba za su yi gaggawar alakanta hatsarin da rashin kyawun yanayi ba.

Tuni aka gano na’urar nadar bayanai na jirgin wato Black Box da za ta taimaka wajen gano musabbabin aukuwar hatsarin.

Shekaru bakwai kenan da kera jirgin wanda kamfanin Saratov Airlines ya siya daga hannun wani takwaransa shekara guda da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.