Isa ga babban shafi
Rasha

Jirgin fasinja a Rasha ya yi hatsari

A yau Lahadi wani jirgin Fasinjan Rasha  ya yi hatsari dauke da mutane 71.Jirgin ya yi hatsari ne dab da birnin Moscow na kasar ta Rasha.Jami’an agaji sun soma isa a inda  jirgin saman fasinjan kasar Rasha ya yi hatsari . 

Jirgi kirar Antonov na kasar Rasha.
Jirgi kirar Antonov na kasar Rasha. ( Photo : Wikimedia.org)
Talla

Ofishin hukumar dake sa ido  zuwa batutuwa da suka shafi zirga -zirga jiragen sama ya bayyana cewa babu wata sheida dake nuna  ko jirgin ya samu tangardar na'ura  bayan da ya cira daga filin tashi na Domodedovo.

Jirgin ya kama da wuta kafin ya rufta kasa a wani yanki mai suna  Argounovo  a kudu maso gabacin kasar.

Wannan jirgi kirar Antonov  An-148 na dauke da mutane 71.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.