Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya nemi Rasha ta kawo karshen ukubar da ake ciki a Syria

Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya bukaci takwaransa na Rasha Vladimir Putin da ya taimaka wajen kawo karshen ukubar da fararen hula ke fuskanta a Syria sakamakon hare-haren da gwamnatin Bashar Al assad ke kaiwa kan sansanin 'yan tawaye.

Akalla fararen hula 220 hare-haren sojin Syria suka hallaka, banda wadanda dakarun Amurka suka kashe.
Akalla fararen hula 220 hare-haren sojin Syria suka hallaka, banda wadanda dakarun Amurka suka kashe. REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Wata tattaunawa da shugabannin biyu suka yi ta waya, an ruwaito shugaba Emmanuel Macron na rokon shugaba Vladimir Putin da ya yi iya bakin kokarinsa wajen kawo karshen wahalar da fararen hula ke fuskanta a gabashin Ghouta da Idlib.

Shugba Macron ya ce ya kadu da samun labarin amfani da makami mai guba na Chlorine akan fararen hula a lokuta da dama.

Ministan Tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian ya ce shaidun da su ke da su, sun nuna cewa anyi amfani da makamin, amma ministan tsaro Florence Parly ta ce har yanzu suna gudanar da bincike don tantancewa.

Rahotanni sun ce akalla fararen hula 220 hare-haren sojin Syria suka hallaka, banda wadanda dakarun Amurka suka kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.