Wata tattaunawa da shugabannin biyu suka yi ta waya, an ruwaito shugaba Emmanuel Macron na rokon shugaba Vladimir Putin da ya yi iya bakin kokarinsa wajen kawo karshen wahalar da fararen hula ke fuskanta a gabashin Ghouta da Idlib.
Shugba Macron ya ce ya kadu da samun labarin amfani da makami mai guba na Chlorine akan fararen hula a lokuta da dama.
Ministan Tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian ya ce shaidun da su ke da su, sun nuna cewa anyi amfani da makamin, amma ministan tsaro Florence Parly ta ce har yanzu suna gudanar da bincike don tantancewa.
Rahotanni sun ce akalla fararen hula 220 hare-haren sojin Syria suka hallaka, banda wadanda dakarun Amurka suka kashe.