Isa ga babban shafi
Maldives

Yameen ya ki ganawa da kasashen EU kan rikicin Maldives

Shugaban Maldives Abdulla Yameen, ya ki ganawa da jakadun Kasashen Turai da suka halarci kasar a karon farko tun bayan da ta tsindima cikin rikicin siyasa na baya-bayan nan.

Shugaba Abdulla Yameen na Maldives
Shugaba Abdulla Yameen na Maldives REUTERS
Talla

Shugaba Yameen da ya cafke manyan alkalai da ‘yan adawar kasar a cikin wannan makon, ya ki sauraren jakadun Kungiyar Tarayyar Turai da Jamus da Birtaniya da suka halarci kasar a wannan Alhamis.

Tsibirin Maldives ya fada cikin rikicin siyasa ne bayan shugaba Yameen ya ki mutunta umarnin kotun koli na sakin fursunonin siyasa tara, in da kuma ya yi gaban kansa wajen kafa dokar ta baci a sassan kasar.

Jakadan Jamus a Sri Lanka, Jorn Rohde ya ce, abin bakin ciki ne kan yadda gwamnatin Maldives ta kaurace wa zaman tattaunawa da jakadun na Turai, kuma ya ce, hakan ba zai haifar da da mai ido ba.

Baya ga zargin murkushe ‘yan adawa, har ila yau, gwamnatin Maldives ta dakatar da kafafen yada labaran kasashen ketare, in da ta sanya tsauraran sharuddan samun Bisar shiga kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci shugaba Yameen da ya janye dokar ta bacin da ya kafa, yayin da Kwamitin Sulhu na Majalisar ke shirin gudanar da taron sirri a yau don tattaunawa kan rikicin na Maldives.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.