Isa ga babban shafi
Amurka

Rundunar hadaka ta kashe mayaka 100 a Syria

Rundunar hadaka da Amurka ke jagoranta a yakin Syria ta sanar hallaka mayaka 100 da ke goyon bayan sojin Syria a wani hari da ta kai mu su a lardin Deir al-Zor.

Wasu daga cikin sojin Amurka da ke yaki da mayakan ISIS
Wasu daga cikin sojin Amurka da ke yaki da mayakan ISIS THOMAS COEX / AFP
Talla

Amurka ta ce, harin kan sojojin na Syria ya zama tilas domin kare nata kawayen wato mayakan Kurdawa na YPG da Syrian ke shirin kai wa hari don kwace yankunan da ke karkashinsu, wadanda suka karbo mu su daga hannun mayakan kungiyar IS a baya.

Harin na Amurka ya zo ne a dai dai lokacin da dangantaka ta kara yin tsami tsakaninta da gwamnatin Bashar al-Assad bisa zargin sa da amfani da makami mai guba wajen kai wa yankunan ‘yan tawaye hare-hare da suka yi sanadin hallakar daururwan fararen hula da jikkata wasu da dama.

Kafin kai harin na safiyar yau, wani jami’in sojin Amurka da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, kimanin mayaka masu biyayya ga gwamnatin Syria akalla 500 ne suka kai hari kan wasu kayayyakin aikin hakar mai da Iskar gas a sassan lardin na Dier Ezzor cikin dare a jiya Laraba.

Kuma a cewar Hedikwatar Sojin Amurka, akan idanun wasu jami’anta ne sojin Syrian da mayakan da ke mara mu su baya suka kaddamar da harin kan mayakan na Kurdawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.