Isa ga babban shafi
Belgium-France

Kotun Belgium na tuhumar maharin birnin Paris

An tsaurara matakan tsaro a duk fadin kasar Belgium a daidai lokacin da Salah Abdeslam, mutum daya daga cikin maharan birnin Paris a shekara ta 2015 da ya tsira da rayuwarsa ke sake gurfana a gaban kotun birnin Brussels a wannan litinin.

Salah Abdeslam ya ki bada hadin kai wajen binciken harin birnin Paris na 2015 ya kashe mutane 130
Salah Abdeslam ya ki bada hadin kai wajen binciken harin birnin Paris na 2015 ya kashe mutane 130 AFP/POLICE NATIONALE/AFP
Talla

Abdeslam mai shekaru 28 a duniya, da aka dauke shi cikin tsauraran matakan tsaro daga wani gidan kurkuku da ke Faransa zuwa Belgium, ana tuhumar sa da yunkurin kashe jami’an tsaro da kuma mallakar makamai ba a kan ka’ida ba.

Matukar dai aka same shi da laifi, Abdeslam da kuma wanda aka kama su cikin gida daya  tare mai suna Sofiane Ayari, za a iya daure su tsawon shekaru 40 kowannensu.

Harin birnin Paris da kungiyar ISIS ta dauki alhakin kaddamarwa a wancan lokaci ya yi sanadiyar mutuwar mutane 130, yayin da masu shigar da kara na Faransa suka yi amanna cewa, Abdeslam ya taka gagarumar rawa a harin amma ya ki bai wa masu bincike hadin kai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.