Isa ga babban shafi
KOREA TA AREWA

Korea ta Arewa ta karya takunkumin da ke kanta

Wani rahoton sirri na Majalisar Dinkin duniya ya ce, Korea ta Arewa ta karya takunkumin da aka kakaba ma ta, in da ta fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare da kudinsu ya kai Dala miliyan 200. Rahoton ya kuma kara da cewa kasar ta samar da makamai a kasashen Syria da Myanmar.

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-un
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-un 路透社
Talla

Rahoton da kafar yada labarai ta Rueters ta ce ta gani, ya nuna cewa kasar ta fitar da makamashin Kwal zuwa kasashen Rasha da Chana da Korea ta Kudu da Malaysia da kuma Vietnam ta hanyar amfani da takardu masu kunshe da bayanai na bogi.

Rahoton ya kuma ambato wata kasa da ba a bayyana sunanta ba wadda ta ce, tana da kwakkwarar shaida kan cewa Korea ta Arewa ta samar da makamai ga kasar Myanmar.

Rahoton ya zargi Korea ta Arewa da ke ci gaba da karya takunkuman da Majalisar Dinkin Duniyar ta kakaba ma ta ta hanyar amfani da hanyoyin safarar mai da ba su dace ba da kamfanonin bayan fage da kuma tsarin bankuna na duniya.

Tun a shekara ta 2006, kasashe 15 na kwamitin sulhu a Majalisar Dinkin Duniya suka samar da wadansu matakai na shake duk wasu hanyoyin samar da kudi ga kasar, domin dakushe kaifin shirinta na sarrafa makamashin nukiliya da kuma miyagun makamai.

Daga cikin abubuwan da aka haramta wa Korea ta Arewa fitarwa sun hada da makamashin kwal da dalma da tufafi da danyen mai da kuma tataccen man fetur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.