Isa ga babban shafi
Amurka

Donald Trump ya bukaci hadin kan al’ummar Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci hadin kan al’ummar kasar domin abinda ya kira sake gina ta da kuma kare iyakokin ta daga duk wata barazanar dake iya tasowa.

Donald Trump Shugaban Amurka
Donald Trump Shugaban Amurka Evan Vucci/AP
Talla

Yayin da yake jawabin sa na farko a zauren Majalisa, shugaban ya tabo cigaban da ya ce an samu ta fannin tattalin arziki inda ya bukaci Majalisa ta karfafa dokokin dangane da shigar baki kasar.

Shugaban ya tabo abinda ya kira barazanar da Koriya ta Arewa ke yiwa Amurka ,Trump ya dau alkawali na cigaba da amfani da sansanin Guantanamo.

Shugaban ya ce babu yadda zasu samu nasara ba tare da bangarorin siyasar kasar sun hada kan su domin yin aiki tare ba.

Jam’iyyar Democrat ta mayar da martini nan take kan jawabin da shugaba Donald Trump yayi inda ta bukaci Amurkawa su ci gaba da jure kura kuran da ake tafkawa a karkashin wannan gwamnati domin yin amfani da zabe na gaba wajen daukar mataki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.