Isa ga babban shafi
faransa-syria

Faransa ta sanya wa wasu kamfanoni takunkumi saboda Syria

Faransa ta kakaba wa wasu kamfanoni da mutane 25 takunkumi bisa zargin suna da hannu a hare-hare da aka kai a Syria da makamai masu guba. Matakin na Faransa ya bada damar kwace kadarorin mutanen da kamfanonin da suke kasuwancin kayayyakin lantarki, tama da karafa da kuma safarar jiragen ruwa.

Kananan yara na cikin wadanda hari makami mai linzami ya hallaka a Syri
Kananan yara na cikin wadanda hari makami mai linzami ya hallaka a Syri Omar haj kadour / AFP
Talla

Mafi akasarin attajirai da kamfanonin da takunkuman suka shafa na zaune ne a Beirut da Damascas da kuma Paris, sai kuma wani dan kasar China guda.

Ko da yake Faransa, Amurka da kuma Majalisar Dinkin Duniya sun dade suna zargin gwamnatin Bashar al Assad da amfani da makamai masu guba, wajen kai wa ‘yan tawayen Syria hare-hare, babu ko da mutum guda daga manyan mukarraban gwamnatin kasar da sunansa ya fita a cikin wadanda Faransa ta kakabawa takunkuman.

Hakan kuwa na da nasaba da rashin gamsassun shaidu da ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta ce ba ta da su kan jami’an gwamnatin ta Syria.

Faransa ta kiyasta cewa daga shekarar 2012 zuwa 2017 da ta gabata, an kai hare-hare da makamai masu guba da suka salwantar da rayukan fararen hula masu yawan gaske a sassan Syria har sau 130.

Ko a ranar Litinin da ta gabata, kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce, fararen hula 21 da suka hada da kananan yara, sun yi fama da matsalar numfashi bayan harin da makamai masu guba da aka kai a wani yankin ‘yan tawayen Syria da ke wajen Damascus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.