Isa ga babban shafi

Rasha ta musanta zargin Amurka a kan Koriya

Rasha ta musanta zargin da Amurka ke yi mata na taimakawa koriya ta Arewa domin cire takunkuman karayar tattalin arziki da aka kakabamata. Sanarwar da fadar gwamnatin kasar ta fitar ta ce wannan zargi bashi da tushe.

Shugaba Donald Trump na Amurka ya zargi Rasha da taimakawa Koriya ta Arewa
Shugaba Donald Trump na Amurka ya zargi Rasha da taimakawa Koriya ta Arewa Reuters
Talla

Sanarwar da Rasha ta fitar na biyo bayan zargin da shugaba Trump ya yi wa kasar da taimakawa Koriya ta Arewa wajen gani an cire takukumai da kasashen duniya suka kakabawa kasar da kuma bai wa Pyongyang duk kayayyakin da China ta daina shigarwa kasar.

Trump da ke zantawa da kafar yadda labaran Reuters ya nuna takaicinsa da kasar da ya ke gani zai iya kula kawance bayan nasaran da ya samu a zaben 2016. A cewar shugaban Rasha ba ta ba da hadin-kan da ya dace kan koriya ta arewa.

Koriya da ke ci gaba da kasancewa babban kalubalin da Trump ke fuskanta, shugaban ya bayyana shakunsa kan ko tattaunawa da Kim Jong-un na koriyan zai yi amfani la’akari da taurin kan da kim ke nunawa a ci gaba da kwajin makamin nukiliya.

Trump ya daura laifi kan shugabanni Amurka da suka gabata Bill Clinton da Geaorge W. bush da kuma Barack Obama na gaza shawo kan wannan rikici.

Kasashen China da Rasha dai duk sun sanya hannu nuna amincewarsu da matakin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya kakabawa kasar Karin Takukumai a shekara da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.