Isa ga babban shafi
Italiya

An ceto bakin haure dubu 1,400 a tekun Mediterranean

Dakarun tsaron gabar ruwan Italiya sun ceto bakin haure kimanin dubu 1 da 400 a tekun baharu-rum da ke kokarin tsallawa zuwa nahiyar Turai, in da biyu daga cikinsu suka rasa rayukansu.

'Yan Afrika da dama na ci gaba da kasadar tsallakawa zuwa Turai ta tekun Mediterranean
'Yan Afrika da dama na ci gaba da kasadar tsallakawa zuwa Turai ta tekun Mediterranean REUTERS/Hani Amara
Talla

Rundunar yaki da miyagun fatauci a teku ta kungiyar kasashen Turai da kungiyoyin agaji sun taimaka wajen ceto mutanen da kawo yanzu ba a fayyace asalin kasashen da suka fito ba.

Dubban ‘yan asalin nahiyar Afrrika na kasadar tsallakawa zuwa Turai, yayin da dama daga cikinsu ke rasa rayukansu a kai akai.

A cikin wannan shekarar kadai, kimanin ‘yan cirani 974 ne suka isa Italiya ta tekun Mediterranean kamar yadda ma’aikatar cikin gidan Italiya ta sanar duk da cewa, an samu karancin masu kokarin isa Turai idan aka kwtanta da bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.