Harin kunar bakin wake ya kashe mutane 35 a Bagadaza
Akalla mutane 35 sun rasa rayukansu a wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake a birnin Bagadaza na Iraqi kamar yadda majiyar likitoci ta sanar.
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar cikin gidan kasar ta ce, wasu mutane biyu ne sanye da jigidar bama-bamai suka kai harin na yau a dandalin Tayaran.
Harin shi ne na biyu a cikin kwanaki uku, yayin da sama da mutane 90 suka samu rauni.
Tun lokacin da mayakan ISIS suka mamaye wasu yankuna a shekarar 2014 a Iraqi, birnin Bagadaza ke fama da hare-haren bama-bamai.
Sai dai an samu sassaucin farmakin bayan sanarwar da gwamnatin kasar ta bayar da ke cewa, ta karbe dukkanin wuraren da ke karkashin ikon ISIS a watan jiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu