Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya sha alwashin kawar da shirin DACA

Shugaban Amurka Donald Trump ya jaddada kudurinsa na ganin ya kawar da shirin bayar da kariya ga kananan yara 'yan gudun hijira da suka shigo kasar ba bisa ka’ida ba da aka fi sani da DACA, wanda tsohon shugaban kasar Barrack Obama ya assasa.

A cewar Trump shirin na DACA wanda Barack Obama ya assasa na taka muhimmiyar rawa wajen haddasa kwararowar baki Amurka.
A cewar Trump shirin na DACA wanda Barack Obama ya assasa na taka muhimmiyar rawa wajen haddasa kwararowar baki Amurka. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

A wasu jawabai da ya wallafa yau Lahadi a shafinsa na Twitter, Trump ya ce ba zai dakata ba har sai ya ga ya kammala murkushe shirin na DACA mai bayar da kariya ga kananan yara ‘yan gudun hijira da suka shigo Amurka.

Matakin na Trump na zuwa ne kwana guda bayan hukumar shige-da fice ta sanar da dawo da fara rijistar shirin ga sabbin yaran da suka shigo Amurka, bayan umarnin da wata babbar kotun kasar ta bayar na ci gaba da bayar da kariya ga kananan yaran da suka shigo kasar don samun mafaka.

Bayan daukar tsawon lokaci kotun na nazarin batun a Talatar da ta gabata ta fitar da umarnin dakatar da yunkurin na Trump kan shirin na DACA inda ta ce shirin baya tattare da wata illah kuma yana kan doron doka.

Sai dai kuma a martinin na Trump a yau, ya ce ba zai sauraraba har sai ya ga karshen shirin wanda a cewarsa yana bayar da dama ga yara musamman daga makwabtan kasar Nahiyar Afrika dama gabas ta tsakiya wajen kwarara tare da cin gajiyar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.