Isa ga babban shafi
Faransa- China

Faransa da China sun cimma yarjeniyoyi kan kasuwanci.

Shugaba Xi Jinping na China da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron, sun bayyana farin cikinsu dangane da yarjeniyoyin da aka cimma tsakanin kasashen biyu, musamman ta fannin kasuwanci. Macron ya bayyana ziyarar da cewa, ta taimaka sosai wajen samar da daidaito ta fannin cinikayya a tsakanin kasashen biyu.

O presidente francês Emmanuel Macron e o anfitrião, Xi Jinping,em 8 de janeiro de 2018.
O presidente francês Emmanuel Macron e o anfitrião, Xi Jinping,em 8 de janeiro de 2018. REUTERS/Ludovic Marin/Pool
Talla

Macron ya ci gaba da cewa doli ne su samar da daidaito ta fannin kasuwanci a tsakaninsu, inda yace anafuskantar karancin yan kasuwar kasar China dake zuba jari a Faransa sabanin yadda Fransawa ke zuba jari mai yawa a China.

Wannan ya sa mu yin nazari sosai domin tantance bangarorin da muke ganin cewa, ya fi dacewa mu saka jari a ciki.

A kowace shekara muna sayo hajoji na kimanin Euro bilyan 40 daga China, amma abinda mu ke sayar wa kasar sam bai kai wannan adadi ba.

A lokacin wannan ziyara mun tattaunawa da mahukuntan kasar a siyasance kan wannan batu, kuma na yi kokarin ganin cewa tattaunawar ta haifar da sakamakon da kowane bangare ai amfana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.