Isa ga babban shafi
jiragen sama

An samu ƙarancin hadduran jiragen sama a 2017

Wani rahoton hukumar kiyaye hadurran jiragen sama ta ƙasa da ƙasa ASN ta ce, an fi samun karancin hadurran jiragen sama a shekarar 2017 fiye da ko yaushe. Hukumar ta ce an samu ci gaban ne duk da karuwar jigilar jiragen saman a bana.

Wani hatsarin jirgin sama a 2017
Wani hatsarin jirgin sama a 2017 REUTERS/Vladimir Pirogov
Talla

Munanan hadurran jiragen sama har sau 10 aka samu, wadanda suka yi sanadin hallakar fasinjoji 79 a cikin shekarar 2017, idan aka kwatanta da shekarar 2016, in da a cikinta aka samu aukuwar munanan hadurran jiragen saman sau 16 tare da asarar rayuka 303.

Hukumar ta ce, cikin bayanan hadduran da suka tattara, har da na kananan jirage masu daukar fasinjoji 14.

Rahoton ya ce, mafi munin hadarin shekarar 2017 ya auku ne cikin watan Janairu, lokacin da wani jirgin saman Turkiya na dakon kaya ya fada kan wani kauye a Kyrgyzstan in da ya hallaka baki dayan ma’aikatan jirgin 4 da wasu mutane 35 da ke kasa.

Sai kuma hadarin jiirgin da ya fadi a yammacin Costa Rica mai dauke da fasinjoji 208, in da 12 daga ciki suka hallaka, hadarin kuma ya auku ne a yayin da ake dab da bikin shiga wannan sabuwar shekara.

Sai dai wannan rahoton bai tattara alkalumman da suka shafi hadurran jiragen saman sojoji da na masu saukar ungulu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.