A cikin wata sanarwa da ya fitar, Mr Guterres ya ce rikice-rikice sun rincabe, haɗurra sun ƙaru, sannan barazana game da yaɗuwar makaman ƙare-dangi ta yi zafi mafi muni cikin shekarun nan.
Sanarwar ta ƙara da cewa duniya na fuskantar gagarumin take haƙƙokin bil’adama da rarrabuwar kawuna.
A saboda haka ne shugaban na majalisar ɗinkin duniya ya yi kira da a haɗa kai domin ganin yadda za ciyar da duniya gaba da kuma zamowa mafaka ga dukkanin bil’adama.