Isa ga babban shafi
Amurka

Mutane 12 sun hallaka sakamakon Gobara a New York

An tabbatar da mutuwar mutane 12 ciki har da yara kanana 4 sakamakon gobarar da ta tashi a wani gini da ke Bronx a birnin New York na Amurka.Tuni dai aka fara bincike domin gano musabbabin tashin gobarar, a wannan gini da ke kunshe da iyalai 25 a cikinsa.

Gobara a Bronx dake birnin New York na kasar Amurka
Gobara a Bronx dake birnin New York na kasar Amurka /REUTERS/Amr Alfiky
Talla

Gobarar da ta tashi a jiya Alhamis , ta mamaye fadin ginin dake kunshe da iyalai 25 a  Bronx dake  birnin na New york.                                                                                                                              Jami’an ceto sun ce gobarar ta tilasta kwashe daruruwan mutane daga gidaje. Mai’akatar kashe gobarar Amurka ta ce wannan shekara ta 2017 ta kasance shekarar da suka samu yawan gobara kama daga ta daji zuwa gobarar gidaje, dan karamin lisafi ya nuna daga farkon wannan shekara zuwa yanzu, gobarar daji ta kone fadin kasa da ya zarce kadada miliyan 7.1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.