Isa ga babban shafi
Rasha

Hukumar zaben Rasha ta yi watsi da takarar jagoran ‘yan adawa

Hukumar zabe a Rasha ta yi watsi da bukatar da jagoran ‘yan adawa Alexei Navalny ya gabatar domin tsayawa takara a zaben shugabancin kasar na shekara mai zuwa don fafatawa da Vladimir Putin.

Alexei Navalny jagoran yan adawa na kasar  Rasha
Alexei Navalny jagoran yan adawa na kasar Rasha REUTERS/Tatyana Makeyeva
Talla

Dukkanin mutane 12 da ke da hurumin jefa kuri’a a hukumar zaben ne suka yi watsi da takarar Navalny, inda suka kafa hujjar cewa an taba yanke ma sa hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari saboda samun sa da almundahna da dukiyar kasar.

A makon da ya gabata ne Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya bayyana cewar zai tsaya takarar zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa wanda zai bashi damar samun karin shekaru 6 a karagar mulki.

Shugaba Putin ya sanar da haka ne lokacin da ya kai ziyara wani kamfanin man kasar, inda ya ce zai gabatar da kan sa a matsayin dan takarar zaben da za’ayi a watan Maris na shekara ta 2018.

Idan ya samu nasara, Putin zai ci gaba da mulki zuwa shekara ta 2024.

Shugaba Putin ya hau karagar mulki a shekarar 1999 inda ya jagoranci Rasha zuwa shekara ta 2008 da ya mikawa Dmitry Medvedev, ya kuma zama Firaminista.

A shekarar 2012 Putin ya sake dawowa shugaban Rasha inda ya taimakawa kasar bunkasa tattalin arzikin ta duk da takunkumin da kasashen Turai suka kakaba mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.