Majalisar Dinkin Duniya ta yi watsi da matsayin Amurka
Majalisar Dinkin Duniya da gagarumar rinjaye ta yi watsi da matsayin Amurka na bayyana Birnin Kudus a matsayin babban birnin Israila.Duk da barazanar janye tallafi da Amurka ta yiwa kasashen duniya, kasashe 128 suka kada kuri’ar watsi da matsayin na Amurka.
Wallafawa ranar:
Kasashe 128 suka kada kuri’ar kin amincewa da matsayin na Amurka daga cikin kasashen duniya 193 dake Majalisar,yayin da kasashe 9 suka ki,kana kasashe 35 suka kauracewa kada kuri’a.
Cikin kasashen da suka goyi bayan Amurka, sun hada da Guatamala da Honduras da Togo, yayin da kasashe irin su Argentina da Canada da Mexico da Philipines da Romania da Rwanda suka kauracewa kada kuri’a.
Jakadiyar Amurka Nikki Haley ta bayyana cewa babu abinda zai canja dangane da matsayin Amurka.
Amurka za ta sanya ofishin jakadanci ta a Birnin Kudus, shine abinda Amurkawa suke so, kuma shine matakin da ya dace a cewar Halley.
Wakilin Falesdinu a Zauren ya bayyana vewa
sun hadu ne ba da manufar kiyaya ba ga Amurka, sai dai don tabbatar da gaskiya da kuma abinda ya dace wanda kasashen duniya suka amince da shi
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu