Isa ga babban shafi
Faransa

Mahmud Abbas ya gana da shugaba Macron kan kafa kasar Falasdinu

Shugaban Falasdinawa Mahamud Abbas ya gana da Shugaban Faransa Emmanuel Macron a birnin Paris, inda Shugabanin biyu suka tattauna dangane da nasarar da aka cimma sa’o’I kadan bayan kada kuri’ar watsi da matsayar Trump a Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas lokacin da ya ke gaisawa da takwaransa na Faransa a ziyarar da ya kai birnin Faris don yaba musu kan jajircewarsu wajen watsi da matsayar Trump kan birnin Qudus.
Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas lokacin da ya ke gaisawa da takwaransa na Faransa a ziyarar da ya kai birnin Faris don yaba musu kan jajircewarsu wajen watsi da matsayar Trump kan birnin Qudus. Francois Mori / POOL / AFP
Talla

Mahmud Abbas wanda ya kaddamar da wani rangadi na musamman ga wasu kasashen duniya don nuna gamsuwarsa gare su dangane da yadda suka yi watsi da matsayar Trump game da ayyana Qudus a matsayin babban birnin Isra'ila tare da neman goyon bayansu kan kafa kasar Falasdinu.

A jawabin da shugaban na Faransa Emmanuel Macron ya gabatar, ya ce zai yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin an ci gaba da samun zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Emmanuel Macron da ya ke magana dangane da batun kafa kasar Falasdinu, ya ce baya tunanin hakan zai samar da maslaha tare da kawo karshen takaddamar da ake fuskanta tsawon shekaru.

Haka Zalika shugaban ya ce ba zai goya baya ga duk wani yunkurin haddasa rikici tsakanin al'umma ba.

Macron ya kuma yi mummunar suka ga Amurka wadda ya ce ta zubar da girma da kimarta a Idon Duniya, musamman dangane da barazanar da ta yi na janye tallafi ga duk wata kasa da ta kada kuri'ar kin amincewa da matsayarta yayin kada kuri'ar kan hakan a Majalisar Dinkin Duniya.

A baya dai Mahmud Abbas ya yi ikirarin cewa matukar Trump ya ki janye matsayarsa kan birnin na Qudus babu shakka zai nemi amincewar kasashen duniya wajen kafa kasar Falasdinu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.