Isa ga babban shafi
MDD

MDD ta yi gargadi kan illar kayayakin wutan lantarki

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan illar da kayayakin wutan lantarki da aka dai-na amfani da su ke haifar wa a duniya, inda ta bukaci samo hanyar sa ke sarrafa su domin magance matsalar.

Wayoyin Salula na cikin Kayayaki wutar lantarki da ke illar ga bil'adama
Wayoyin Salula na cikin Kayayaki wutar lantarki da ke illar ga bil'adama Getty Images / Bloomberg
Talla

Wani rahotan hadin-guiwa na Hukumar kula da sadarwa ta Majalisar da kungiyar sarrafa shara at duniya ya bayyana cewar akalla tan kusan miliyan 45 na irin wadannan kayayakin wuta aka samu a shekarar 2016, wanda idan aka tara shi wuri guda tsayin sa yafi tsaunin Eiffel Tower mai tsayin kafa 4,500 a birnin Paris.

Rahotan ya ce nan da shekarar 2021, duniya za ta cika da irin wadannan sharar kayayakin wutar lantarki da zai kai tan miliyan 52 da suka hada da na’urar wanki da talabijin da fanka da wayar salula da firji.

Houlin Zhao, shugaban hukumar sadarwa ta duniya ya ce wadannan kayayaki na fitar da sinadarin da ke da hadari ga rayuwar Bil Adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.