Adadin ƴan Jaridun da ake ɗaurewa a shekara ya tashi-CPJ
Ƙungiyar da ke kare haƙƙoƙin ƴan Jaridu ta duniya, CPJ ta ce, adadin ƴan Jaridun da aka ɗaure a shekarar 2017 ya sake tashi, in da sama da rabin su suka fito daga ƙasashen Turkiya da China da kuma Masar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahotan ƙungiyar na shekara da ta fitar a yau, ya nuna cewar ƴan Jaridu 262 aka tsare a cikin wannan shekara, wanda ya zarce na bara 259.
Rahotan ya ce, Turkiya da China da Masar kawai sun ɗaure 134 wanda ya zarce kashi 51 cikin 100 na bana.
Alkaluman sun nuna cewar Turkiya ta ɗaure ƴan Jaridu 73,in da China ta daure 41 a bana, yayin da Masar da ta daure 20.
Ana yawan cin zarafin ƴan Jaridu a yayin gudanar da ayyukansu na sanar da al’umma kan halin da duniya ke ciki, in da wani lokacin su ke rasa rayukansu, yayin da wasu ke samun rauni baya ga lalata kayayyakin aikinsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu