Isa ga babban shafi
Muhalli

Kasashen duniya za su rage zubar da robobi

Kasashen Duniya sama da 200 sun amince su dauki matakin rage zubar da robobi da magungunan da ke gurbata iska da ruwan sha da koguna da kuma kasar noma, a wajen taron magance gurbata muhalli na Majalisar Dinkin Duniya da aka kamala a Nairobi.

Kasashen Duniya sama da 200 sun amince su dauki matakin rage zubar da robobi
Kasashen Duniya sama da 200 sun amince su dauki matakin rage zubar da robobi Brent Lewin/Bloomberg via Getty Images
Talla

Taron na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewar sauya halayyar mutanen da ke amfani da robobin da kuma masu sarrafa su na da matukar muhimmanci wajen kare muhalli daga gurbacewa.

Mahalartar taron sun ce gurbacewar muhalli na rage rayuwar miliyoyin mutanen duniya kowacce shekara, abinda ya sa ya zama dole ga gwamnatocin kasashen duniya su dauki mataki a kai.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla kowacce rana mutane 9 daga cikin 10 kan shakar gurbatacciyar iskar da ke kashe mutane 17,000.

Mataimakin Daraktan Hukumar kula da Muhalli ta Majalisar, Ibrahim Thiaw ya ce ganin yadda matsalar ta ke da girma, ya zama wajibi mutane su bai wa gwamnatoci hadin-kai domin kawo karshen matsalar.

Jami’in ya ce alkaluma sun nuna cewar kowacce shekara ana jibge tsakanin tan 5 zuwa 13 na robobi a cikin teku wanda ke illa ga mutane da kuma hallitun da ke ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.