Isa ga babban shafi
Kudus

Kasashen duniya sun kalubalanci matakin Trump kan Kudus

Shugabannin Kasashen duniya na ci gaba da bayyana rashin amincewar su da matakin da shugaba Donald Trump na Amurka ya dauka a birnin Kudus.

Donald Trump a lokacin da ya ke ayyana birnin Kudus a matsayin birnin Isra'ila
Donald Trump a lokacin da ya ke ayyana birnin Kudus a matsayin birnin Isra'ila REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ke ziyarar Algeria ya bayyana matakin a matsayin abin takaici, inda ya bukaci kaucewa tashin hankali.

Macron ya ce Faransa da kungiyar kasashen Turai na nan kan bakar su na samun kasashe biyu tsakanin Israila da Falasdinu dake zama kusa da juna.

Firaministan Birtaniya Theresa May ta ce gwamnatin Birtaniya ba za ta amince da matakin na Amurka ba wanda ta ce ba zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya ba.

Shugabar diflomasiyar kungiyar kasashen Turai Federico Mogherini ta ce ta hanyar tattaunawa ne kawai za a warware rikicin Gabas ta tsakiya.

Kasashen Saudi Arabia da Turkiya da Jordan da Masar da Syria duk sun yi watsi da matakin na Amurka wanda suka ce ya sabawa dokokin duniya.

Tuni kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira taron gaggawa ranar juma’a domin tattauna matsayin shugaba Trump wanda tuni ya haifar da zanga zanga a kasashen larabawa.

Kasashe 8 da suka hada da Bolivia da Birtaniya da Faransa da Italia da Senegal da Sweden da Uruguay suka bukaci gudanar da taron.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Alla-wadai da matakin inda ya ke cewa ta hanyar tattaunawa ne kawai za a warware matsalar Israila da Falasdinu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.