Isa ga babban shafi
Amurka

Birnin Qudus:Trump na kan bakarsa

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da Sarki Abdallah na Jordan da kuma shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas cewa, ko shakka babu zai dauke ofishin jakadancin kasar daga Tel Aviv zuwa birnin Qudus, matakin da ke matsayin share fage ga Isra’ila domin karbe birnin baki dayansa daga Falasdinu.

Shugaban Amurka Donald Trump zai gabatar da jawabi kan matsayinsa game da dauke ofishin jakadacin kasar daga Tel Aviv zuwa birnin Qudus
Shugaban Amurka Donald Trump zai gabatar da jawabi kan matsayinsa game da dauke ofishin jakadacin kasar daga Tel Aviv zuwa birnin Qudus REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Shugabannin kasashen Larabawa sun gargadi matakin dauke ofishin jakadancin na Amurka daga Tel Aviv zuwa birnin Qudus, in da suke ganin cewa, hakan ka iya harzuka Musulmai.

Yahudawa da Falasdinawa na girmama birnin Qudus a matsayinsa na wuri mai tsarki duk da sabanin da ke tsakaninsu.

Isra'ila na kallon Qudus a matsayin babban birninta, yayin da Falasdinawa ke kallon  gabashin Qudus a matsayin babban birnin kasar da  Falasdinu ke fatan ayyanawa nan gaba.

Amurka ce dai kasa ta farko da ta ke shirin aiwatar da matakin dauke ofishin jakadancin daga Tel Aviv zuwa birnin Qudus.

Wani lokaci a yau ne ake saran shugaba Trump zai gabatar da jawabi kan wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.