Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

Taron cutar HIV na gudana a birnin Abidjan

An shiga rana ta biyu a ci gaba da gudanar da taron shekara-shekara dangane da yaki da cutar HIV ko kuma Sida a birnin Abidjan na kasar Cote d’Ivoire, taron da zai ci gaba da gudana har zuwa ranar Asabar mai zuwa.

Cutar HIV na ci gaba da barazana ga rayukan jama'a a sassan duniya
Cutar HIV na ci gaba da barazana ga rayukan jama'a a sassan duniya AFP PHOTO/ Manjunath KIRAN Manjunath Kiran / AFP
Talla

Sama da wakilai dubu 10 ne daga sassa daban daban na Afrika ke halartar wannan taro da aka saba gudanarwa a kowace shekara, cikinsu kuwa har da Michel Sidibe daraktan zartarwa na hukumar yaki da cutar Sida a duniya.

Har ila yau akwai masu ruwa da tsaki da kuma shugabannin hukumomin da ke yaki da wannan cuta kamar Dr. Matshidiso Moeti dan kasar Malawi, wanda ke shugabanci hukumar lafiya ta duniya reshen Afrika.

Ivory Coast dai na daya daga cikin kasashen Afirka da wannan cuta ke ci gaba da yaduwa, in da aka bayyana cewa kashi 4% na al’ummar kasar ne ke dauke da kwayoyin cutar ta HIV.

Taron dai na daga cikin bukukuwan da ake gudanarwa a kowace shekara domin tunawa da ranar yaki da wannan cuta a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.