Isa ga babban shafi
Isra'ila

Matsayin Trump kan mayar da Qudus fadar Isra'ila

Shugaban Amurka Donald Trump ya jinkirta bayyana matsayinsa dangane da shirin da Isra’ila ke yi na dauke fadar gwamnatin kasar daga Tel Aviv Zuwa birnin Qudus.A wata sanarwa da ta fitar jiya Litinin, kungiyar kasashen Musulmi ta duniya ta yi gargadi dangane da irin abubuwan da za su iya biyo bayan ayyana birnin na Quds a matsayin fadar gwamnatin Isra’ila.

Shugaban Amurka Donald Trump da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Shugaban Amurka Donald Trump da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Mai magana da yawun fadar gwamnatin Amurka White House Hogan Cidley ya ce, shugaban ya jinkirta bayyana matsayinsa dangane da wannan mataki kamar yadda aka tsara a jiya Litinin, matakin da zai bai wa Amurka damar fara tsara yadda za ta dauke ofishin jakadancinta daga Tel Aviv zuwa Quds a cikin watanni 6 masu zuwa.

To amma ba wai hakan na nufin cewa Trump ya jingine wannan batu baki daya ba ne, domin sanarwar ta ce, shugaban zai bayyana matsayinsa a wani lokaci nan gaba.

A wata sanarwa da ta fitar a jiya litinin, kungiyar OIC wadda ta kunshi kasashen musulmi 57 ta ce, duk wani yunkuri na ayyana birnin Qudus a matsayin fadar gwamnatin Isra’ila, abu ne dai zai yi matukar harzuka Musulmi da kuma Larabawa a duniya.

Shi ma shugaban Faransa Emmanuel Macron, a wata zantawa da ya yi ta wayar tarho jiya Litinin, ya bayyana wa Donald Trump fargabarsa dangane da irin sakamakon da wannan mataki zai iya haifarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.