Isa ga babban shafi

Yawan masu kamuwa da Maleriya sun karu-WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce sama da mutane dubu 445 ne suka rasa rayukansu a fadin duniya cikin shekarar 2016, sakamakon kamuwa da cutar ta zabbabin cizon sauro.

WHO ta ce sai an yi da gaske za a iya magance cutar maleriya nan da 2030
WHO ta ce sai an yi da gaske za a iya magance cutar maleriya nan da 2030 REUTERS/James Gathany
Talla

Rahoton hukumar ya ce an samu karuwar yawan wadanda ke kamuwa da cutar cizon sauron da akalla mutane miliyan biyar, daga mutane miliyan 211 da bincike ya nuna cutar Maleriya ta shafa a shekarar 2015

Bayanin rahoton ya tabbatar da cewa miliyan 57 da dubu 3 da cutar da addaba sun fito ne daga Najeriya kadai.

WHO ta ce a halin yanzu ana bukatar ware sama da akalla dala biliyan 6 da dubu 500 nan da zuwa shekarar 2020, domin kawo karshen cutar cizon sauro a shekarar 2030.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.