Isa ga babban shafi
Bosnia

Praljak ya kwankwadi guba a gaban kotun duniya

Kotun duniya da ke birnin Hague ta dakatar da zaman sauraren shari’ar Slobodan Praljak da ake zargi da aikata laifukan yaki a Bosnia bayan ya kwankwadi guba. Mr. Praljak ya kwankwadi gubar ne bayan Kotun ta goyi bayan hukuncin daurin shekaru 20 da aka yanke ma sa.

Slobodan Praljak, lokacin da ya ke kwankwadar guba a gaban kotun duniya da ke yanke ma sa hukuncin daurin shekaru 20 a gidan kaso
Slobodan Praljak, lokacin da ya ke kwankwadar guba a gaban kotun duniya da ke yanke ma sa hukuncin daurin shekaru 20 a gidan kaso REUTERS
Talla

Bayan Kotun duniyar ta goyi bayan garkame shi a gidan kaso har na tsawon shekaru 20, Slobodan Praljak mai shekaru 72 ya fito da wata karamar kwalba dauke da gubar da ya kwankwada, bayan ya yi ta fadin cewa, shi ba mai laifi ba ne, kuma ba zai amince da hukuncin ba.

Jim kadan da wannan al’amari mai ban al’ajabi, alkalin kotun Carmel Agius ya bada umarnin dakatar da zaman shari’ar Praljak, sannan kuma aka sauke labulayen da ke kewaye da dakin kotun.

Wakilan Kamfani Dillancin Labaran Faransa na AFP sun shaida yadda a cikin ‘yan mintina motar daukan marasa lafiya ta iso harabar kotun ta Hague, yayin da jirgin sama mai saukar ungulu ke ta shawagi a sararin samaniya.

Kazalika ma’aikatan jinya da dama dauke da jakkuna a bayansu sun yi gaggawar kutsawa cikin Kotun amma alkalai suka bukaci a kwantar da hankali.

Sai dai rahotanni na baya-bayan na cewa, likitoci sun yi nasarar yi ma sa magani.

Ana tuhumar Praljak da laifin bada umarnin rushe gadar birnin Mosta na Bosnia mai dimbin tarihi a cikin watan Nuwamban shekarar 1993, yayin da alakai suka bayyana rushe gadar a matayin babbar barna ga fararen hula Musulmi a Bosnia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.