Isa ga babban shafi
KOREA TA AREWA

Mun mallaki cikakken makamin nukiliya- Jong Un

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya bayyana cewa, kasarsa ta mallaki cikakken karfin makamin nukiliya bayan sabon gwajin makami mai linzami a ranar Talata, wanda ya ce, ka iya riskar daukacin Amurka.

Shugaban Korea Ta Arewa Kim Jong-un da jami'an gwamnatinsa na duba wani nau'in makamin nukiliya
Shugaban Korea Ta Arewa Kim Jong-un da jami'an gwamnatinsa na duba wani nau'in makamin nukiliya KCNA via REUTERS
Talla

Gwajin dai ya kasance na farko cikin watanni biyu da suka gabata, kuma yazo ne mako guda da Amurka ta malkaya wa Korea ta Arewan wasu jerin takunkumai, in da kuma ta shigar ta sunan kasar cikin sunayen kasashen da ke taimaka wa taaddanci.

Takunkuman na Amurka kan Korea ta Arewa sun shafi harkan sufurin jiragen ruwa, duk dai domin tilasta wa Korea ta Arewan jingine gwaje-gwajen makamai da aka hana ta.

Babban Hafsan Sojin Korea ta Kudu ya gaskata cewa, makamin da Korea Ta Arewa ta chilla ya tsallake gabashin gunduman kudancin Pyongyang.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi Allah wadai da sabon gwajin makamin, yayin da ya bukaci kasar ta kawo karshen takalar da ta ke yi.

A yau ake saran Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da taron gaggawa kan gwajin don daukan mataki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.