Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 20/08 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 20/08 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 20/08 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 20/08 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 20/08 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 20/08 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 20/08 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/08 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 20/08 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/08 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 20/08 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Najeriya

Shi'a ta roki MDD da ICC kan Zakzaky

media Mabiya Shi'a dauke da hoton jagoransu, Sheik Ibrahim al-Zakzaky AFP PHOTO PIUS UTOMI EKPEI

Kungiyar ‘yan Shi’a a Najeriya ta roki Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai da Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika da kuma Kotun Duniya da su tsoma baki wajen ganin cewa, gwamnatin Najeriya ta saki jagoransu, Sheik Ibrahim al-Zakzaky da matarsa da ke tsare kusan shekaru biyu.

Shugaban Kwamitin gagwarmayar sakin Zakzaky, Sheik Abdulhamid Bello da ke zantawa da manema labarai a birnin Kaduna ya ce, suna son kuma a tono gawarwakin mabiya Shi’a 347 da aka binne a wani a wani katafaren kabarin bai daya don yi mu su jana’iza irin ta addinin Musulunci.

Sheik Bello ya bukaci kafa wani kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike game da zargin da suke yi wa sojin kasar kan kisan kiyashin mabiya Shi’a a garin Zaria a shekarar 2015.

A cewar Bello “ ana ci gaba da tsare shugabanmu ba tare da tuhumarsa ba da kuma bada damar ganawa da shi har tsawon shekaru biyu duk da cewa shekara guda kenan da babbar kotu ta bayyana matakin tsare shi a matsayin wanda ya saba doka da keta hakkinsa, sannan kuma ta bada umarin sakin sa ba tare da wasu sharudda ba”.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure