Isa ga babban shafi
Lebanon

Sa'ad Hariri mai murabus ya koma Lebanon

Firaministan Lebanon mai murabus Sa’ad Hariri ya isa birin Beirut a karon farko tun bayan da ya sanar da matakinsa na yin murabus sama da makwanni biyu a Saudiya.

Firaministan Lebanon mai marabus Sa'ad Hariri kewaye da jami'a tsaro a birnin Beirut
Firaministan Lebanon mai marabus Sa'ad Hariri kewaye da jami'a tsaro a birnin Beirut REUTERS/Mohamed Azakir
Talla

Jim kadan da isowara filin tashi da saukan jiragen sama na Beirut, Mr. Hariri ya samu kyakkyawar tarba daga jami’an tsaron kasar.

Ana ganin cewa, Hariri ya jefe Lebanon cikin rikicin siyasa sannan ya ce, ya yi murabus daga kujerarsa, matakin da ya bai wa ‘yan kasar matukar mamaki.

Shugaban Lebanon, Michel Aoun ya ki amincewa da murabus din Hariri daga Saudiya har sai ya gana da shi gaba da gaba.

Ana saran shugabannin biyu za su gana da juna wani lokaci a yau.

Firaministan ya musanta zargin cewa, Saudiya ce ta tilasta ma sa komawa Lebanon don ta ci gaba da nuna gogayyar karfi da Iran a yankin kasashen Larabawa.

Ana saran Hariri ya fayyace matsayinsa kan lamurran siyasar Lebanoan a yau kamar yadda ya alkawaranta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.