Hariri zai koma Lebanon a makon gobe
Firaministan Lebanon mai murabus Sa’ad Hariri ya bayyana cewa, zai koma birnin Beirut nan da kankanin lokaci don halartar bikin ranar samun ‘yancin kasar a ranar Laraba mai zuwa.
Wallafawa ranar:
Wannan na zuwa a yayin da kasar ta fada cikin rikicin siyasa tun bayan da ya sanar da matakinsa na yin murabus a Saudiya.
Hariri ya sanar da shirinsa na komawa Lebanon ne bayan ganawarsa da shugaban Faransa Emmanuel Macron a birnin Paris a yau Asabar.
Mr. Hariri ya kara da cewa, zai taka rawa a bikin samun ‘yancin kan kasarsa, sannan kuma zai sanar da matsayarsa akan lamurran siyasar kasar bayan ganawar da zai yi da shugaba Michel Aoun.
Shugaban Faransa Emmanuel Macrona na kokarin samar da matsalaha ce game da rikicin siyasar Lebanon.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu