"Yarjejeniyar EU da Libya kan bakin-haure abin takaici ce"
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana yarjejeniyar da kungiyar kasashen Turai EU ta kulla da Libya, domin hana baki kwarara nahiyar Turai ta tekun Meditareniya a matsatyin abin takaici, saboda yadda ake cin zarafin bakin.
Wallafawa ranar:
Shugaban hukumar kare hakkin Dan Adam ta majalisar Zeid Ra’ad Al Hussein, ya bayyana damuwa kan azabar da bakin-hauren ke fuskanta, a wuraren da ake tsare da su a Libya.
Jami’in yace babu yadda za’a yi kasashen duniya su zuba ido suna kallon irin cin zarafin da bakin ke fuskanta a Libya.
Hukumar dake yaki da bakin a kasar ta Libya, tace yanzu haka tana tsare da baki 19,900 daga kari kan 7,000 na watan jiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu