Isa ga babban shafi
Saudiyya

An kama mutane 201 kan zargin almundahana a Saudiyya

Kasar Saudi Arabia ta ce ana yi wa mutane 201 tambayoyi dangane da zargin rashawa da barnata dukiyar kasa wanda ya kai na kudi dala miliyan dubu 100.

Saudiyya ta ce tana kokarin tsaftace al'amuran kasar daga rashawa.
Saudiyya ta ce tana kokarin tsaftace al'amuran kasar daga rashawa. Reuters/路透社
Talla

Hakan na zuwa ne yayin da gwamnatin kasar ke kokarin kawar da gurbatattun mutane daga cikin manya-manyan kasar.

‘Yayan sarautar kasar, da ministoci, da kuma hamshakan ‘yan kasuwa ne ke cikin jerin manyan masu fada a ji da aka damke ko kuma aka kora daga aiki, yayin da yarima Muhammad Bin Salman ke kokarin kankame madafun iko.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar yada labaru ta kasar ta ce an riga an sallami mutane 7 bayan da aka ji ta bakinsu.

Ma’aikatar ta ce akwai alamun cewa al’amarin rashawa a kasar ya munana.

Gwamnatin kasar ta kulle asusun ajiya na mutanen da ake zargi, sannan kuma ta yi gargadin cewa za a kwace kadarori mallakin wadanda ake zargin.

Ta kara da cewa binciken da aka gudanar cikin shekaru uku da suka gabata sun bayyana cewa an yi wandaka da kudin gwamnati wadanda suka kai dala miliyan dubu 100.

Wannan dai shi ne mataki mafi girma da hukumomi a kasar ta Saudiyya suka dauka wajen yaki da rashawa.

Matakin dai na zuwa ne yayin da kasar ta Saudi Arabia ke fama da rikice-rikice a yankin larabawa, inda Saudiyyar ke takun-saka da kasar Iran dangane da wani makami da aka harbo zuwa cikin kasar daga Yemen. Da kuma cece-ku-cen da ya barke bayan murabus din firaministan kasar Lebanon, wanda ya sanar a birnin Riyadh.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.