Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta daina karbar bakin haure daga kasashe 11

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce gwamnatinsa za ta dakatar da shirinta na karbar bakin hauren da suka fito daga wasu kasashe 11 na dan lokaci, wadanda ta bayyana da mafi hadarin kasashe. Sanarwar da fadar gwamnatin kasar ta fitar ta ce galibin kasashen da za su fuskanci wannan dakatarwa na daga yankunan Afrika da gabas ta tsakiya.

A cewar Trump, matakin na daga cikin yunkurin da gwamnatinsa ke yi na ganin ta tabbatar da tsaro da kuma kare kasar daga ayyukan ta'addanci.
A cewar Trump, matakin na daga cikin yunkurin da gwamnatinsa ke yi na ganin ta tabbatar da tsaro da kuma kare kasar daga ayyukan ta'addanci. REUTERS/Joshua Roberts
Talla

Matakin na Amurka na zuwa ne a dai dai lokacin da wasu kasashe ke amincewa da ci gaba da karbar ‘yan ciranin tare da samar da shirye-shiryen da za su inganta rayuwarsu.

A cewar sanarwar gwamnatin za ta samar da wani tsari da zai taimaka wajen hada iyalan da ke cikin ‘yan ciranin da tun da farko suka shigo Amurka ta yadda za a fara tantancewa da kuma tsananta bincike kan iyalan da ke neman shigowa.

Wani babban jami’in gwamnatin ya ce sauye-sauyen na daga cikin kokarin da gwamnatin Trump ke yi na inganta tsaron kasar tare da kare ta daga ayyukan ta’addanci.

A jiya Talata ne dai wa’adin kwanaki 120 da shugaba Trump ya bayar don haramta kwararowar karbar bakin hauren ya kammala, inda kuma ya fitar da sabuwar sanarwar umarnin na wannan sabon tsari.

Kasashen da hanin ya shafa sun hadar da Misra da Iran da Iraqi da Libya da Mali da Korea ta arewa da Somalia da Sudan da kuma makwabciyarta Sudan ta kudu, sauran sun hada da Syria da kuma Yeman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.