Isa ga babban shafi
Isra'ila

Isra'ila ta soke tattaunawa da Falasdinawa saboda Hamas

Gwamnatin Israila ta ce, ba za ta tattauna da kungiyar Falasdinu ba muddin tana kunshe da kungiyar Hamas mai dauke da makamai har sai kungiyar ta ajiye makamanta tare da  amincewa da kafuwar Isra'ila.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. REUTERS/Sebastian Scheiner/Pool
Talla

Majalisar tsaron Isra'ila ta amince da wannan matsayi bayan wani taro da ta gudanar sakamakon hadewar da kungiyar Fatah ta Falasdinawa ta yi da Hamas mai mulkin Gaza.

Isra'ila ta gindaya wasu sharudda da ta ce, dole sai Hamas ta amince da su, kafin su hau kujerar tattaunawa wadanda suka hada da amincewa da kafuwar Isra'ila da kuma ajiye makaman kungiyar da kuma shaida wa duniya cewar ta yi watsi da ayyukan ta’addanci.

Ofishin Netanyahu ya ce, Isra'ila ba za ta tattauna da Falasdinu ba saboda Hamas

Har ila yau, Isra'ila ta bukaci daina karbar duk wani tallafi daga Iran wadda ke taimaka wa rundunar sojinta, kana da mikawa Isra'ilar wasu sojojin ta guda biyu da suka bata a Gaza da kuma wasu fararen hula uku da aka ce suna fama da tabin hankali.

Ya zuwa yanzu Hamas dai bata mayar da martani akai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.