Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Amurka na barazanar janyewa daga yarjejeniyar nukiliyar Iran

Wani lokaci a wannan juma’a shugaban Amurka Donald Trump zai bayyana matsayinsa dangane da yarjejeniyar da kasashen duniya suka kulla da Iran kan shirin kasar na nukiliya.

Ministocin harkokin wajen kasashen duniya bayan kulla yarjejeniya da Iran a watan yulin 2015
Ministocin harkokin wajen kasashen duniya bayan kulla yarjejeniya da Iran a watan yulin 2015 REUTERS/Joe Klamar/Pool
Talla

Trump dai ya ce bai amince da abubuwan da ke kunshe a yarjejeniyar wadda gwamnatin Barack Obama ta amince da ita a shekara ta 2015 ba.

 

Matakin na shugaban zai bai wa ‘Yan Majalisa damar yin mahawara a kai da kuma daukar matakin sanya wa kasar ta Iran sabbin takunmai.

 

Tuni kungiyar Turai tare da kasashen Birtaniya, Faransa, China, Jamus da kuma Rasha suka ce su kam suna nan kan yarjejeniyar da suka kulla.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.