Isa ga babban shafi
libya

An kama 'yan cirani sama da dubu 3 a Libya

Dakarun da ke kawance da hadakar gwamnatin Libya wadanda ke yaki da ayyukan fasa-kauri akan iyakokin kasar sun ce, cikin karshen makon nan kadai sun kama sama da ‘yan cirani dubu 3 da ke kokarin shiga kasar ba bisa ka’ida ba.

Wasu daga cikin dakarun Libya da ke yaki da fasa-kaurin mutane
Wasu daga cikin dakarun Libya da ke yaki da fasa-kaurin mutane TAHA JAWASHI / AFP
Talla

A cewar kwamamdan rundunar Bassem Ghrabli, sun yi nasarar kama masu tsallakowa kasar ba bisa ka’ida ba kimanin dubu 3 da 150 da suka kunshin ‘yan Asiya da Larabawa da kuma wasu ‘yan kasashen Afrika.

Ghrabli ya ce, dakarun sun gudanar da wani samame kan masu fasa-kaurin karkashin jagorancin tsohon shugaban ‘yan fasa-kaurin a wajen birnin daya kai su tsawon makonni uku ana yi.

Rikicin dai ya kai ga rasa rayukan kimanin mutane 39 yayin da wasu 300  suka jikkata, in da kuma makarantu da asibitoci da dama suka lalace.

Kazalika hukumar bunkasa ilmin kimiyya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce an lalata muhimman wuraren tarihi da ke yammacin birnin Tripoli mai nisan kilomita 70 daga Sabratha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.