Isa ga babban shafi
Amurka

Tillerson ya musanta sun taba samun sabani da Trump

Sakataren harakokin wajen Amurka Rex Tillerson ya musanta bayanan da ke cewa a wani lokaci can baya, mataimakin shugaban kasar ya rarrashe shi domin hana shi yin marabus daga mukaminsa.

Sakataren harakokin wajen Amurka Rex Tillerson tare da shugaban Amurka Donald Trump
Sakataren harakokin wajen Amurka Rex Tillerson tare da shugaban Amurka Donald Trump ©REUTERS/Kevin Lamarque/File Photo
Talla

A cewarsa ko da wasa, ba wata rana da mataimakin shugaban kasa ya rarrashe shi domin ci gaba da kasancewa sakataren harkokin waje, saboda bai taba cewa zai yi marabus ba.

Tillerson ya shugaban Trump, mutum ne mai kishin Amurka, har kullum Amurka da kuma al’ummarta ne mafi muhimmanci a wajensa.

"Amma akwai wadanda ke neman kawo cikas ga manufofin ci gaba da Trump ke son aiwatarwa, ni ba na cikinsu kuma ba zan taba kasancewa a cikinsu ba", in ji Tillerson.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.