Rahotan da Cibiyar yaki da cutar kansa ta wallafa ya ce kasha 71 na Amurkawa na fama da kibar da ta wuce kima, kuma alkalumman sun nuna cewar mutane 630,000 da ke fama da cutar kansar na da irin wannan kibar.
Daraktan hukumar Brenda Fitzgerald ya ce wadanda ba su dauke da wannan cutar yanzu haka, suna fuskantar barazanar kamuwa da ita saboda kiba.
Fitzgerald ya ce yin kibar da ta wuce kima na haifar da cututuka 13 da ke da nasaba da kansa da suka hada da kansar makogwaro da kumburi a wuya da kansar nono da koda da kuma hanta.
Rahotan ya ce kashi biyu bisa uku na mutane 630,000 da suka kamu da cutar a shekarar 2014 na tsakanin shekaru 50 zuwa 74. Rahotan ya kuma ce mata sun fi hatsarin kamuwa da irin wannan cuta.